Da wata kasuwar baje kolin kayan abincin noma da kiwo ne aka fara wannan taro da ke matsayin wata hanyar tattara matsalolin manoma da makiyaya da a dai gefe damuwar mutanen dake aiyukan sarrafa kayan abinci don sayarwa a ci gaba da shirye shiryen babban taron MDD na shekara-shakara.
Mme Zeinabou Hamani ta kungiyar Agri-Focus na daga cikin wadanda suka shirya wannan taro. Ta kuma ce mahimmacin taron shi ne don a gano matsalolin da manoma da makiyaya ke fuskanta don a samu mafita.
Ko ya mahimmancin taron yake a wajen masu sarrafa kayan abincin noma da kiwo ? Mme Yacouba Aichatou Amadou na sana’ar sarrafa nono, ta kuma bayyana wa muryar Amurka cewa suna kawo kayan ne wajen baje kolin don a sansu kuma su samu sana'ar yi ba sai sun dogara ga mazajensu ba.
Wannan yunkuri na zuwa ne a wani lokacin da illolin Canjin yanayi ke kara tsananta a kasashen Sahel irinsu jamhuriyar Nijer.
Hukumar samarda wadatar cimaka ta kasa wato Initiatiive 3N da ka fi sani da‘yan Nijer su cida ‘yan Nijer it ace ke kan gaban wannan taro na share fagen zuwa tarorakin da ake saran gudanarwa a nan gaba a birane Roma da New York don duba hanyoyin tallafawa kasashe masu tasowa inda baya ga canjin yanayi matsalar ta haddasa tsayarwa aiyuka a karkara. Aboubacar Aboubacar Oumarou shine darektan sashen dake kula da abinci mai gina jiki a hukumar 3N.
Bayan wannan baje koli na tsawon wuni 1 taron zai ci gaba da maharori a wuni na 2 da na 3 domin cimma matsayar da za a tunkari babban taron MDD na watan satumba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5