Ta hanyar wannan ganawa Shugaba Mohamed Bazoum na son karfafa dangantaka a tsakanin gwamnati da kungiyoyin fararen hula.
Jami’an farar hula masu goyon bayan gwamnati da wadanda suka yi fice wajen sukar manufofin gwamnatin ne suka halarci wannan zama domin jin ta bakin shugaban kasa.
Da suke maida martani ga bukatar ta shugaban kasa wadanan jami’ai sun gabatar da takardar bukatun da suke dauka a matsayin mafitar matsalolin Nijer da jama’arta.
Shugabar kungiyar ABC ta masu faffitika ta hanyar Blogue Samira Sabou ta yi amfani da wannan haduwa don jan hankula a game da masu kokarin shafawa kungiyoyin fafitika kashin kaji.
Wannan shine karon farko da wani shugaban kasar Nijer ke kiran taron tantaunawa da shugabanin kungiyoyin fararen hula a tsawon shekaru 30 na mulkin dimokradiya, abinda ake ganinsa a matsayin wani babban yunkurin da zai taimaka a kawo karshen tsamin dangantakar da aka yi fama da ita a takanin gwamnatin da ta gabata da wadanda ke kiran kansu ‘yan rajin kare dimokradiya.
Saurari cikakken rahoton souley Mummuni Barma cikin sauti: