Daruruwan mutane galibinsu mata da yara da tsofafi ne wasu a mota wasu a amalanke wasu a kafa ke gudun hijira zuwa garin Tilabery a karshen makon nan, sakamakon abin da suka kira yanayin tashin hankalin da ake ciki a karkarar Anzourou, inda ‘yan bindiga suka kaddamar da hare hare ba kakautawa a wani lokacin da aka yi zaton kura ta lafa akan iyakar Nijar da kasashen Mali da Burkina Faso.
A cewar magidanci Almoustapha Seini, kowa ya fice daga kauyen Zeibane haka Koira-Tegui ba kowa Gadabo haka-zalika a yanzu haka mutanen Gasa da Tunkusa da kauyukan dake wannan yanki sun kama hanyar yin hijira.
Ita kuwa dattijuwa Mariama Hamidou cewa take abin da ya tura kusu wuta ya fi wuta zafi. Ta ce dole ne su tsere kasancewar ana yiwa mutane yankan rago tare kone runbunan abincinsu.
Yanzu haka Hukumomin Nijar sun samarwa da ‘yan gudun hijirar masauki a filin kokawa na Tilabery, a matsayin sansanin wucin gadi. Yanzu haka dai suna samun kulawar da ta dace kafin a samu damar daukar matakan mayar da su gidajensu.
Sai dai yayin da mahukunta ke yunkurin mayar da wadanan mutane inda suka fito wani mazaunin kauyen Zibane Koira Zeino Alpha Soumana na ganin abin ba zai yi tasiri ba muddin ba a dauki matakin sintiri mai dorewa ba.
Matsalar tsaro a jihar Tilabery wani abu ne da za a iya cewa tamkar ana magani kai yana kaba ganin yadda ‘yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka duk kuwa da cewa yana daya daga cikin yankunan dake karkashin dokar ta baci ba’idin dubban sojojin cikin gida da na waje dake jibge akan iyakar Nijer Mali da Burkina faso a karkashin rundunonin G5 Sahel da Minusma da Barkhane.
Hari na baya-bayan nan shine wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 10 a karkarar Anzourou a ranar da aka yi shaglugulan karamar sallah.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.