Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Bubaci Gwamnatin Njar Ta Biya Dan Fafatuka Diyya


ECOWAS
ECOWAS

Kotun ECOWAS ta umurci hukumomin jamhuriyar Nijer su biya diyyar million 50 na cfa domin shafe hawayen wani dan gwagwarmayar kasar da ya shafe watanni 18 a kurkuku bayan da ya kira wani gangamin nuna adawa da dokar harajin kasar a shekarar 2018.

Kotun ta kuma gargadi gwamnatocin kasashen G5 Sahel da na Afrika ta yamma su daina fakewa da matsalar tsaro don hanawa jama’a morar ‘yancin zanga zanga.

A watan Afrilun 2018 ne gwamnatin shugaba Issouhou Mahamadou ta kama Sadat Iliya Dan Malan na kungiuar MPCR bayan da ya jagoranci zanga zangar watsi da wata sabuwar dokar harajin 2018 a Damagaram saboda a cewarsa dokar ba ta yi dai dai da yanayin rayuwar al’umar Nijer ba.

Bayan shafe shekara 1 da rabi ana kai ruwa rana a kotunan cikin gida lauyoyinsa suka garzaya kotun ECOWAS a watan satumban 2019 wace a zamanta na larabar da ta gabata ta bayyana matsayinta game da wanann kara.

Me Boudal Effred shine lauyan Sadat Iliya Dan Malan. Ya kuma ce dole ne gwamnati ta biya Sadat hakkin shi na miliyan 50 nan da wata uku sannan kuma ta tura takardar da ta nuna hakkan.

Kama ‘yan adawa da jami’an kungiyoyin farar hula a yayin gudanar da zanga zanga ko wani gangamin kalobalanatar mahukunta wani abu ne da ya zama ruwan dare a kasashen yammacin Afrika da na G5 Sahel saboda abinda suke kira dalilan tsaro sabili kenan kotun ECOWAS a yayin wannan zama ta gargadi gwamnatoci su daina fakewa da wannan matsala don rufe bakin jama’a.

Shugaban kungiyar MPCR na kasa baki daya Alhahji Nouhou Mahamadou Arzika ya yaba da wannan hukunci na kotun CEDEAO domin a cewarsa mataki ne da ke kara wa dukkan ‘yan gwagwarmayar Afrika karfin aiki.

Duk kokarin da wakilin Muryar Amurka ya yi na jin matsayin hukumomin Nijer akan wannan hukunci bai yi nasara ba domin kakakin gwamnati Tidjani Abdoulkadri da sakataren gwamnati Abdou Dan Galadima da na tuntuba ta waya ba wanda ya daga wayarsa haka kuma ba su maido min amsar sakon sms din da na aika masu ba har zuwa lokacin aika wannan rahoto.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

XS
SM
MD
LG