Nijar: Kawancen jam'iyyun hamayya sun ziyarci Hamma Ahmadou a kurkuku

Hamma Ahmadou shugaan jam'iyyar MODEN LUMANA da zai fafata da shugaban kasa a zaben zagaye na biyu

Yayinda zaben shugaban kasar Nijar zagaye na biyu ke karatowa shugabannin gamayyar jam'iyyun siyasa da suke goyon bayan Hamma Ahmadou a zaben mai zuwa sun kai masa ziyara a kurkuku

Kusan duka manyan shugabannin kawancen jam'iyyun hamayya da ake kira COPA suka kai wa Hamma Ahmadou ziyara a gidan kaso inda yake tsare bisa wani zargi da bashi da alaka da siyasa a cewar gwamnatin kasar

Wadanda suka kai masa ziyara sun hada da Muhammad Usman da Seni Umaru da Umaru Noma shugaban kiron kwarya na MODEN LUMANA da duk masu fatan ganin Hamma Ahmadou ya doke shugaban kasa Mahammad Issoufou a zaben zagaye na biyu wanda za'a yi ranar 20 ga wannan watan..

Dalilin ziyarar itace na tabbatar masa cewa sun dauki duk matakan da zasu bashi damar doke abokin karawarshi shugaban kasa Issoufou.

Shugaban jam'iyyar PNPD Intinikar Alhassan na cikin tawagar ta COPA, wannan kawance mai goya wa Hamma Ahmadou baya. Shi ya bayyana yadda aka ki barinsu ganinshi gaba daya. Daga bisani an barsu su dinga shiga ganinsa biyar biyar kuma minti biyar kacal aka ba kowane gungu.

Sun ganshi cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali duk da matsanancin tsaro dake kewaye dashi. Shugabannin suna cewa komi ya sameshi zasu dora alhakin kan gwamnatin Mahammadou Issoufou.

Shugaban jam'iyyar PSD Basira Ben Omar Muhammad mai goyon bayan Mahammad Issoufou ya musanta zargin hukumomi nada hannu a halin da Hamma Ahmadou yake ciki. Yace abun da ya kasihi kurkuku daban yake da zabe. Kada a hada batutuwan biyu wuri daya. Daban suke. Zancen zabe daban zancen aikin ashsha da aka yi kuma daban ne.

A jadawalin zabe ranar 20 ga wannan watan za'a yi zaben zagaye na biyu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Kawancen jam'iyyun hamayya sun ziyarci Hamma Ahmadou a kurkuku - 2 53"