Nijar: Ana Ce-ce-ku-ce Bayan Da Tsohon Shugaba Mahaman Ousman Ya Ba Matarsa Mukami A Ofishinsa

Shugaban Jam’iyyar RDR Canji Alhaji Mahaman Ousman

Wata sabuwar dambarwa ta taso a Jamhuriyar Nijar tsakanin ‘yan adawa da masu mulki bayan da shugaban Jam’iyar RDR Canji Alhaji Mahaman Ousman ya bai wa matarsa mukamin sakatariya a ofishinsa na tsohon shugaban kasa.

NIAMEY, NIGER - A yayin da a bangaren rinjaye ake ganin rashin dacewar wannan nadi, su kuwa ‘yan hamayya na cewa har yanzu ba su manta ba da nade-nade irin na son rai da tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou ya yi a zamaninsa inda ya bai wa ‘dansa mukaman gwamnati sau biyu duk kuwa da cewa akwai ‘ya'yan jam’iyyar PNDS da suka fi shi cancanta.

Tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar Issouhou Mahamadou

Kundin tsarin mulkin Nijar ya yi tanadin wasu muhimman abubuwa irin na karrama ga dukkan wadanda suka taba shugabancin wannan kasa inda bayan maganar albashi da kudaden al’awus da ma’aikatan kula da tsaro doka ta tanadi ofishin musamman domin irin wadanan mutane da ke matsayin uwayen kasa tare da ba su damar zaben hadiman da suka aminta da su.

Ta wannan dalili ne tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman ya nada maidakinsa Hajiya Aichatou Rony a matsayin sakatariyarsa ta dindindin lamarin da ya haifar da mahawara a kafafen sada zumunta musamman a tsakanin ‘yan hamayya da masu mulki, amm wani jigo a jam’iyar RDR Canji Malan Issa Galadima na kare matakin na tsohon shugaban kasa.

Wannan dambarwa ta farfado da wata mahawwara ta daban akan abinda ‘yan hamayya ke kira son kan da tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou ya nuna a zaminsa inda ya fifita iyalinsa fiye da sauran ‘yan kasa a sha’anin tafiyar da lamuran mulki. Sawun da a yanzu haka gwamnati mai ci ke bin sa.

To sai dai wani mai magana da yawun jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki Alhaji Assoumana Mahamadou ya musanta zargin na gwada son kai a tsawon mulkin Mahamadou Issouhou, ya na mai cewa dukkan wadanda ya bai wa mukaman gwamnati shugaban ya yi ne a bisa cancanta.

Nade-naden mukamai na daga cikin matsalolin da ke haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin magoya bayan jam’iyun siyasar Nijar inda sau tari abin kan zama sanadin ballewar wasu ko barkewar rikicin shugabanci.

Saurari cikakken rahoton daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Dambarwa Ta Barke Bayar Da Shugaban Jam’iyyar RDR Ya Baiwa Matarsa Makami A Ofishinsa.mp3