A yayin ganawarsa da shugabanin kungiyoyin farar hula a karshen mako, shugaba Mohamed Bazoum, ya bayyana tabbacin aniyar sa ta daukar matakai domin rigakafin hauhawar farashin ababen masarufi a kasar bayan da a farkon watan nan na Agusta gwamntinsa ta yi karin kudin man diesel sanadiyyar illolin mamayar Rasha a Ukraine.
Matakin na zuwa ne a wani lokacin da al’ummar ta Nijer ke fama da tsadar kayan abinci saboda haka kungiyoyin fafatukar ke cewa suna jiran su gani a kas domin ba zasu laminci dukkan wani matakin da zai kara wa talaka damuwa ba.
Fahimtar da jami'an fafatuka dalilan daukar matakin karin farashin kudin gazoil kokuma man diesel da gwamnatinsa ta sanar a farkon watan nan na Agusta shi ne makasudun wannan taro da shugaban kasa ya kira a fadarsa domin, a cewarsa, hakki ne mahukunta su yi wa ‘yan rajin kare hakkin jama’a bayani a game da irin wannan mataki mai mahimmanci.
Duk da ma ba a gayyaci ‘yan jarida ba, Shugaban kungiyar Voix des sans voix, Nassirou Saidou, na daga cikin wadanda suka halarci wannan zaman.
Kungiyoyin sun bayyana wa shugaban kasa damuwa dangane da abin da ka iya biyo bayan wannan mataki na karin kudin man gazoil ganin yadda tuni kamfanonin sarrafa madara da masu gidajen buga bredi da motocin jigila suka yi karin kudade.
Bayan jin matsayin wadannan ‘yan kare hakkin dan adam, a take Mohamed Bazoum ya basu amsa game da mataki na gaba kamar yadda za a ji a cikin sautin rahoton.
Sai dai shugaban kungiyar MPCR, Alhaji Nouhou Mahamadou Arzika, na ganin an yi riga malan masallaci wajen daukar wannan mataki.
Sabanin yadda gwamnatin Nijar ke danganta karancin man diesel a kasar da mamayar Russia a Ukraine masu mahawara a kafafen sada zumunta na cewa rashin shugabanci nagari a kamfanonin dake kula da harakar mai, wato CNPC da SORAZ da SONIDEP, ita ce matsalar da ke dabaibaye harakoki saboda yadda dalilan siyasa ke zama lasisin da wasu jami’an wadannan kamfanonin ke amfani da shi don azurta kansu a maimakon yi wa kasa aiki kamar yadda har-wa-yau siyasa ta yi dalilin tara dimbin ma’aikatan dake daukar albashi na ba gaira.
Saurari cikakken rahoton Sule Barma: