Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da suke kokarin kakkabe wasu ‘yan bindigar da suka nemi mafaka a mahakar zinaren garin Tamou da ke jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso.
Shugaban hukumar ya gargadi jami’an tsaro da al’umma su hada kai domin cimma nasara a yakin da ‘ake kwafsawa da 'yan ta’adda.
Gwamman mutane ne aka kwantar a manyan asibitocin birnin Yamai a washegarin luguden wutar da jiragen sojan saman Nijar suka yi lokacin da suka bi sawun wasu ‘yan bindigar da suka hallaka ‘yan sanda 2 suka kuma saci makamai a tashar bincike ta garin Tamou a ranar Litinin 24 ga watan Oktoban da ya gabata.
Kwanaki 10 bayan faruwar wannan al’amari, shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH mai shara’a, Maty Alhaji Moussa, da mukarrabansa sun kai ziyara a wadannan asibitoci, domin duba wadanda abin ya rutsa da su.
Moussa ya ce su wajen talatatin aka kawo nan asibitin kasa, amma yanzu sun ce mutane hudu ne suka yi saura, sun ce ana kula da su, kuma nan da kwanaki kadan za a sallamesu.
Rashin fahimta tsakanin jami’an tsaro da al’umma na daga cikin abubuwan da aka gano cewa suna maida hannun agogo baya a yunkurin neman bakin zaren matsalolin tsaro a jihar Tilabery, inda har ma ake zargin wasu talakawa da hada kai da ‘yan ta’adda.
Saboda haka shugaban hukumar CNDH ya gargadi jami’an tsaro da al’ummomin yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula su kasance tsintsinya madaurinki daya.
A sanarwar da ta bayar a washegarin wannan farmaki, ma’aikatar tsaron Nijar ta ce mutane 7 ne suka rasu, sannan 24 suka ji rauni abinda wasu ‘yan kasa suka ce ba gaskiya ba ne, saboda haka kungiyoyin fafutika ke ci gaba da matsa lamba don ganin an gudanar da bincike.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5