Nijar: A Saukaka Ma Talaka Tsadar Makamashi - 'Yan Raji

Bazoum Mohamed

Yayin da makamashi ke dada tsada a Janhuriyar Nijar, 'yan raji sun yi kira ga mahukunta da su rage ma talaka farashin makamashi.

A jamhuriyar Nijar Kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin makamashi sun bukaci hukumomin kasar su kara sassauta harajin na’urori da dukkan kayakin samar da makamashi, ta yadda kayakin samar da wutar lantarki da hasken rana za su zo wa tallaka da sauki kuma a wadace.

Tun a shekarar 2017 ne ma’aikatar kudi ta kasa da ma’aikatar makamashin Nijer su ka dauki matakin sassauta harajin kayayakin samar da wutar lantarki da hasken rana da kuma na’urorin da ke amfani da irin wannan makamashi da duniya ke yunkurin maida hankali akansu fiye da sauran hanyoyin da ake amfani da su a can baya.

Muhawarar OSC 2

To sai dai da alama har yanzu jama’a ba ta fara ganin wani sauyi na Zahiri ba; dalili kenan kungiyoyin fafutika a fannin makamashi suka shirya taron mahawara don tattauna wannan batu. Injiniya a sha’anin makamashi Rabiou Malan Issa jigo ne a kungiyar CODDAE kuma ya yi bayani kamar yadda za a ji a cikakken rahoton idan an dangwali abin sauti.

Darektan kula da sha’anin doka a ma’aikatar makamashi ta kasa, Adamou Amadou, shine aka gayyato domin ya fayyace abinda wannan doka ta sassauta harajin na’urorin samar da makamashi ta kunsa.

Wannan ya sa kungiyoyin fafutika nuna bukatar ganin gwamnatin Nijar ta aiwatar da gyarar fuskar da za ta ba daukacin ‘yan kasa damar shigo da kayakin samar da wutar lantarki ba tare da wata tsangwama ba.

Da yake bayyana nasa matsayin, wakilin hadakar kungiyoyin CSAO, Amadou Dangi, na ganin janye matakan da ya kira shingayen da ke hana wa sauran rukunonin al’umma sukunin amfana da sassaucin harajin da ya shafi kayakin samar da wutar lantarki da na’urorinsu ita ce hanya mafi fa’ida.

Muhawarar OSC 1

Alkaluman ma’aikatar makamashi sun yi nuni da cewa kashi 17 daga cikin 100 na al’ummar Nijar ne ke samun wutar lantarki a yanzu haka alhali gwamnatin kasar ta ayyana fatan cira wa daga wannan matsayi zuwa kashi 85 daga cikin 100 kafin shekarar 2030.

A saurari cikakken rahoton Souleyman Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

KORAFI AKN DOKAR SHIGO DA NA URORIN WUTAR LANTARKI NA ZAMANI .mp3