Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Yankunan Karkara A Najeriya Na Korafi Kan Rashin Ababen More Rayuwa

Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa
Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa

Najeriya na daga cikin kasashen da ke da arziki wanda ya kamata jama'ar ta su more rayuwarsu, sai dai har yanzu alamu na nuna cewa mutane musamman mazauna kauyuka na fama da kishirwa da wasu muhimman ababen more rayuwar.

SOKOTO, NIGERIA - Tun daga Jamhuriya ta daya a Najeriya, yekuwar neman zabe da masu son mukaman dimokradiyya ke yi, ba ta wuce samarwa jama’a ababen more rayuwa kamar ruwa, hanyoyin mota masu kyau, asibitoci da sauransu ba.

Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa
Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa

Yanzu ana shekaru 23 cikin tsarin dimokradiyya wanda bai hadu da katsalandan na Soji ba, kuma tsawon shekarun ana gudanar da shugabanci tun daga matakin shugaban kasa har zuwa na kansila inda ake sa ran jama'a sun amfana da samun ayukka.

Wata ziyara zuwa wasu yankuna na karkara a Jihar Sakkwato dake Arewa maso yammacin kasar ta nuna har yanzu wasu ‘yan kasar na fama da jan ruwa daga riyojin da aka tona na gargajiya.

Wasu masu dibar ruwa daga rijiyar gargajiya suka ce da ruwan ne suke amfanin na rayuwar yau da kullum kamar sha, wanki da wanka har ma da abinci.

Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa
Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa

Duk da hakan jagororin al'umma sun tabbatar da cewa an yi wa jama'a ayukkan samar da ruwa masu tarin yawa.

Shugaban karamar hukumar Gada, Garba Yakubu Tsitse ya ce inda aka fito mutane suna yin dafifi wurin dibar ruwa amma yanzu an samar da riyojin burtsatsi da yawa kuma sun saukaka neman ruwa ga jama'a.

Shi kuwa wani mazaunin karkara Umar Murtala ya ce jama'a na raja'a ga riyojin da ke bude maimakon amfani da wadanda aka samar musu na zamani saboda yawan cinkoson jama'a ga rijiyar burtsatsi wadanda ke aiki.

Wata matala dake tilasta kin amfani da gidajen ruwa na zamani kamar wadanda gwamnatin Sakkwato ta samar masu daukar galon na ruwa miliyan daya da rabi a kananan hukumomin jihar ta ce samun tangarta mai hana gidajen ruwan aiki saboda haka dole jama'a nemi wata hanyar samun ruwa.

Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa
Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa

Murtala Jihadi Illela ma’aikacin sashen injiniyanci na karamar hukumar Illela ya ce gidan ruwa da aka yi musu ya samu tangardar fashewar bututun da ke kai ruwa ga jama'a kuma sun nemi ‘dan kwangila ya gyara amma ba'a gyara ba, hakan ya sa jama'a basu samun ruwa.

A Jihar Sakkwato gwamnatin Jihar da kananan hukumomi sun gudanar da ayyuka masu tarin yawa a bangarorin ilimi , kiyon lafiya, noma, jin dadin jama'a da makamantan su, sai dai duk da haka jama'a na kasancewa cikin yanayin ba koshi ga kwanan yunwa, amma shugaban karamar hukumar Gada Garba Yakubu Tsitse na ganin cewa jama'a ne ba su kulawa da ayyukan da ake yi musu shi yasa wani lokaci ba a morewa ayyukan.

Fatar ‘yan Najeriya da ma na wasu kasashen Afirka da ke gudanar da tsarin dimokradiya bai wuce ganin an gudanar da tsarin ta yadda talaka zai ci ribanta da tsarin ba, abinda aka rasa yanzu a wasu kasashen.

Saurari cikakken rahot daga Muhammadu Nasir:

Najeriya Kasa Mai Arziki Ce Amma Mazauna Kauyuka Na Fama Da Kishirwar Da Ababen More Rayuwa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG