Ziyarar ta ta’allaka ne kan tantance halin da yan gudun hijira suke ciki biyo bayan jerin boren da suka gudanar a sansanin da' yan gudun hijirar ke ciki bayan sun tsere daga tashen tashen hankula a kasashen su.
Gwomman 'yan gudun hijara ne daga kasar Algeria da Libiya ke kwararowa a kowane lokaci zuwa Nijar domin samun mafaka.
Emanuel Gignac jami’in majalisar dinkin duniya mai kula da yan gudun hijirar ya bayyana manufar ziyarar.
Yace "makasudin wannan ziyarar shine domin na gane ma idanu na halin da 'yan gudun hijira ke ciki dama irin tallafin da zamu basu domin kyautata rayuwarsu wanda ya kamata hukumar ta musu. 'Yan gudun hijirar suna da yawan gaske da suka fito daga kasashe daban daban dake samun mafaka a Nijar sakamakon tashe tashen hakulan a kasashen su hukumar ta ware milyan 300 na cfa domin gina musu cibiyar samar da ruwan sha mai tsabta kuma wannan na daga cikin inganta rayuwar yan gudun hijira."
Hukumar tace tana nan tana duba yiwuwar irin tallafin da ya kamata a baiwa 'yan gudun hijirar.
To sai dai a ganawar da shuwagabannin hukumar da su ka yi da kungiyoyin farar fulla kungiyoyin, sun bukaci hukumar ta gaggauta kwashe 'yan gudun hijirar dake jibge a Agadas zuwa kasashen su na asali alkasum mato yan kungiyar farar fulla a Agadas
Yanzu haka de garin Agadas na karbar 'yan gudun hijira fiye da dubu biyu da suka tsere kasashensu da ke fama da tashe-tashen hankula
Saurari rahoton Hamid Mahmoud cikin sauti: