Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Karancin Man Fetur Na Kamari A Wasu Jihohin Najeriya

Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki
Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki

Masu ruwa da tsaki sun koka kan karancin man fetur da ya ki ya ki cinyewa a babban birnin tarayya Abuja da wasu jihohi da dama, duba da cewa ana daf da yin bukukuwan kirsimeti da ma na shiga sabon shekara.

ABUJA, NIGERIA - Wani abu da ya sa aka yi kira ga mahukunta da su tsawata wa Kamfanonin dakon man fetur domin ana zargin sun kara wa litan man fetur kudi wanda ya ke ba bisa ka'ida ba.

Dillalan Man Fetur masu zaman Kansu IPMAN sun yi zargin cewa farashin man fetur zai iya kaiwa Naira 400 lita a mafi yawancin gidajen mai kafin karshen wannan shekarar, sakamakon yadda ake ci gaba da fuskantar karancin man.

Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki
Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki

Dillalan a ta bakin mataimakin Shugaban Kungiyar IPMAN ta kasa Abubakar Maigandi Dakingari sun ce idan karancin man fetur ya gaza raguwa, farashin man fetur zai cigaba da hauhawa saboda sun lura cewa farashin man ya kai kusan Naira 450 lita a kasuwar bayan fage a Jihohi da dama.

Maigandi ya ce an ba MOMAN da DAPMAN da kuma kafofin sayar da man fetur na NNPC ne, su dillalan kuma ana sayar masu a kan lita daya a Naira 215 ko Naira 210 saboda haka zai yi wuya dillalan su saya da tsada kuma su sayar da lita daya akan Naira 170.

Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki
Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da masu ababen hawa irin su Injiya Yaya Mohammed suka yi tir da yadda Gwamnatin taraiyya da kuma Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ke cigaba da yin shiru kan irin wanan karanci da ya dabaibaye bangaren mai.

Yaya ya ce gas ko diesel wadda aka fi sani da AGO shi ne ya yi tsananin tsada har ana sayar da lita daya akan Naira 700 kuma waddanan motoci na dillalan man fetur da shi suke amfani. Yaya ya ce Gwamnanti ti yi kokari a samu wadatar man Diesel, saboda kar karancin man ya durkusad da kasar a lokuta bukukuwan karshen shekara.

Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki
Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki

Daya cikin manyan jami'an Kungiyar Kwadago ta Kasa Kwamred Nasiru Kabir ya ce akwai shawarar da suka ba Mahukuntan kasar a game da wannan matsala ta rashin man fetur tun ba yau ba. Nasir ya ce a yi kokari a gyara matatun man kasar da wuri, kuma Gwamnati ta cigaba da bada tallafi a fanin man fetur, saboda shi ne kawai abinda talaka zai mora.

Ko da yake, Kamfanin man fetur na kasa ya fitar da sanarwa cewa yana da man fetur har lita biliyan 2 a ajiye a gabanin bukukuwan kirsimeti da na karshen shekara ,amma abin jira a gani shi ne ko mahukunta a Najeriya za su dauki shawarar gaggauta gyara matatun man fetur, domin a tace danyen mai a cikin kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Matsalar Karancin Man Fetur Na Kamari A Wasu Jihohin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG