WASHINGTON, DC —
A karo na 7, kungiyar wasan kwallon kafa ta Eyimba, sun gamu da ‘yan fashi da makami ranar litinin din nana da ta gabata akan hanyarsu ta zuwa Kaduna, domin halartar wasanin Lik na kwararrun wato Nigeria Professional Football League NPFL.
Hukumar ta NPFL, ta bayyana cewa fashin ya afku ne a Okene, a yankin tsakiyar Najeriya.
An yima Jami’an da ‘yan wasan kungiyar karkaf amma babu wanda aka jima rauni, kuma wannan fashi ya faru ne da ranan Allah ta’ala, a Okene dake jihar Kogi.
Inda a kayi masu fashi, nan ne aka yiwa Kano Pillars fashi a watan Maris na shekarar ta da gabata a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Owerri, wanda kimanin mutane 5, suka samu raunuka.