Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Wasanni Zai Hadu Da Shugabannin NFF


Barista Solomon Dalung (Igbarman Otarok)
Barista Solomon Dalung (Igbarman Otarok)

Ministan matasa da wasanni na Najeriya Solomon Dalung, ya tabbatar da cewa zai hadu da manyan nan biyu na hukumar wasanni ta Najeriya NFF, a ranar Laraba 20 ga watan nan na Janairu.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta NFF, Amaju Pinnick, na fuskantar suka daga bangaren Chris Giwa tun zaben da aka gudanar cikin watan Agusta na shekara ta 2014.

Sai dai daga bangaren na Giwa an fitar da sanarwar cewa yayi zaton zai fara aiki a matsayin shugaban hukumar ranar 12 ga watan nan, amma Minista Dalung ya shiga cikin maganar inda yace za’a kawo karshen wannan kace nace, har ma yayi bangarorin biyu gargadi da kada su dauki shari’a a hannunsu.

Cikin wani bayani da Minista Salamon Dalung ya fitar yace, “bayan nazarin abubuwan da ke faruwa tsakanin bangarorin biyu, na tsayar da ranar 20 ga watan Janairu, domin mu zauna baki dayanmu mu kawo karshen wannan magana.

An dai shirya wannan yin taron ne ranar Laraba 20 ga watan Janairu, da missalin karfe 8 na yamma.

XS
SM
MD
LG