Bisaga dukkan alamu ‘yan wasanin motsa jikin Najeriya na iya rasa damar su ta shiga gurbi na biyu, a cikin wasannin da aka gudanar na zakarun kasashen Afrika, na shekarar 2015, a dalilin sakamakon wani gwaji da akayi akan ‘yan wasan kasar su 5 da aka samu alamun sunyi amfani da kwayoyin da aka haramtama ‘yan wasa sha.
A jiya Alhamis ne ministan matasa da wasanni Mr. Solomon Dalong ya bayyanar da hakan, a wata ganawa da yayi da shugabanin kwamitin Olympic ta Najeriya.
Ya kara da cewar wasu daga cikin ‘yan wasan sun gaza samun sakamakon wannan gwajin kana wasu kuma daga cikin su, ya bayyana sun sha wasu kwayoyi, a lokacin wasan gasar kasashen Afrika da akayi a garin Wari.
Ministan dai yace rashin bin doka da oda da ‘yan wasan sukayi na iyasa kasar rasa wasu daga cikin tagulla 5 da ‘yan wasan suka samu lokacin gasar.