Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari, ya kara jaddada alkawarin da ya yiwa ‘yan wasan kwallon kafa na Golden Eaglets, da suka lashe kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17, a shekarar 1985, wanda aka gudanar a kasar China.
Shugaban ya furta hakan ne a gidan Gwamnati a Abuja lokacin da yake karbar kyautar hukumar kwallon kafa ta CAF, wanda ‘yan Flying Eagles ‘yan kasa da shekaru 23, suka lashe a kasar Senegal.
Da yake jawabi shugaba Buhari, ya godewa wadanda suka dauki nauyin gasar,yana mai cewa tabbas kwallo na kaunarsa kamar yadda yake son kwallon, kafa saboda a lokacin da yake shugaban Najeriya,a 1985, ne kungiyar ta lashe kofin duniya gashi kuma an sake kwatawa a 201, sun sake lashe kofin duniya.
A nashi jawabin Ministan matasa da wasani Barrister, Solomon Dalung, yace an mika wa shugaban duk kyaututtukan ne saboda kyakkyawan jagorancinsa.