Idan aka duba, wannan ba shine karo na farko da irin wannan lamari ya faru ba, makwanni kadan da suka gabata wasu ‘yan bindiga sun yiwa sojojin kasar Amurka, kwanton bauna inda suka hallaka su.
Ko yaya mazarta kan al’amuran yau da kullum ke kallon lamarin. Sani Rufa’i, masanin halaiyar dan’adam a jihar Damagaran, ya bayyana cewa lamarin nada matukar daure kai, domin kan iyakokin kasashe ne lamarin ke afkuwa.
Masanin ya kara da cewa dakarun manyan kasashen duniya dake sintiri a yankunan nada kayan aiki, misali kama daga jirin sama mara matuki, da manyan bindigogi amma har yanzu an rasa inda wadannan mahara ke fitowa.
Daga karshe ya yi kira da gwamnati ta sake salo wajan daukar matakin magance afkuwar irin wannan tashin hankali da yaki ci yaki cinyewa a wannan bangare na jamhuriyar Nijer.
Daga Jamhuriyar Nijer, ga Tamar Abari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5