An fara samun sabbin bayanai dangane da harin da ya halaka sojojin Amurka dana na Nijar, a dai dai lokcinda wakilan majalisun dokokin Amurka suke tambayar bayanai dangane da harin.
A ranar hudu ga watan nan ne aka kashe sojojin Amurka hudu da hudu na Nijar a wani harin kwanton bauna da akai a wani kauye da ake kira Tongo-Tongo dake kusa da kan iyakar kasar da Mali.
Magajin garin Tongo-Tongo Almou Hassane, ya gayawa Sashen Faransa na MA cewa, sai tayu sojojin sun kwana a arewa maso gabashin Tongo-Tongo.
Sojojin suna farautar wani mai na hanun daman Abu Adnan al-Sahraoui, wani tsohon dan kungiyar MUJAO, wand a ya shiga ISIS a yankin na hamada.
Sojojin sun yi tambayoyi ga kauyawan, wanda ya kai dare fiyeda abunda aka yi tsammani.
Da yake karin bayani, magajin gari Hassane,"yace babu mamaki maharan suna da masu goyon bayansu cikin kauyawan.
An shirya musu gadan zaren ne cewa an kai ko ana shirin kai harin ta'addanci bayan gari, da suka je wurin, tuni dama maharan su 50 ko fi wasu akan babura suka aukwa musu.
Facebook Forum