Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojojin Nijar 12 A Inda Su Ka Kashe Na Amurka 4


Sojojin Amurka da aka kashe a Nijar
Sojojin Amurka da aka kashe a Nijar

Tamkar kashe sojojin Amurka 4 da 'yan ta'addan kasar Mali su ka yi a Janhuriyar Nijar, ya ba su kwarin gwiwar tunanin ashe ma za su iya barnar da ta zarce hakan a daidai wannan lokacin kuma a daidai wurin da su ka aikata barnar baya.

Hukumomi a Janhuriyar Nijar sun ce an hallaka sojojin kasar na musamman akalla 12, a wani hari shigin wanda ya kashe hudu daga cikin sojojin Amurka na musamman da ake kira Green Beret, su ma a Janhuriyar ta Nijar, ran 4 ga watan nan na Oktoba.

Harin na jiya Asabar ya auku ne a wajejen da aka kai hari kan sojojin Amurka, a cewar jami'ai. Su ka ce an kai farmakin na baya baya ne a garin Ayorou, mai tazarar kilomita kimanin 200, arewa maso gabashin Yamai, babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce maharan na dauke da muggan makaman da su ka hada da rokoki da bindigogi. Sun iso wurin ne cikin motoci biyar, inda su ka yi ma sansanin sojojin na musamman kofar rago. Maharan sun arce bayan da sojojin Janhuriyar Nijar su ka kai dauki.

Wurin na daura ne da kan iyakar kasar Mali, inda ake kyautata zaton daga nan ne maharan ke zuwa. Wannan yanki dai na fama da masu ikirarin jahadi cikin 'yan kwanakin nan.

Mutuwar sojojin Amurka hudu, ran 4 ga watan nan na Okotoba, ta janyo gagarumar takaddama a Washington DC, inda 'yan Majalisar Dokoki ke bukatar karin bayani kan al'amarin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG