Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nakiya Ta Kashe Mutane 6 A Somaliya.


Masu zanga zanga kan harin makon jiya a Mogadishu, wanda ya kashe kusan mutane 400.
Masu zanga zanga kan harin makon jiya a Mogadishu, wanda ya kashe kusan mutane 400.

Lamarin ya auku ne lokacinda motar da suke ciki ta taka nakiyar, kamar yadda jami'ai suka fada.

A Somalia farar hula shida sun halaka sakamkon tashin wata nakiya a yau lahadi, kwanaki bayan wani mummunar hari da ya halaka daruruwan mutane.

Jami'ai a yankin kasar da ake kira Lower Shabelle da turanci, sun tabbatarwa Sashen Somaliya na Muriyar Amurka cewa, mata biyu da maza hudu sun mutu bayan wata nakiya irin wadda aka hada a gida ta afkawa wata motar kiya-kiya a kauyen da ake kira Daniga, mai tazarar kilomita 35 daga arewacin birnin Mogadishu.

Mukaddashin gwamnan yankin Ali Nur Mohammed yace wadanda harin ya rutsa da su 'yan kasuwa ne wadanda suke kai amfani gona kasuwa, kuma suna balaguro ne daga gari da ake kira Afgoye zuwa Bal'ad.

Ahalinda ake ciki kuma,limaman addinin Musulunci da suke nan a yankin Washington DC sun yi Allah wadai da mummunar harin ta'addancin da aka kai a Mogadishu da ya kashe kusan mutane 400 da jikkata wasu 228. Limamai da jami'an digilomasiyya sun bayyana bakin cikinsu kan aukuwar lamarin a lokacin sallar Jumma'a.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG