Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamhuriyar Nijar Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Tallafawa Matasa Su Daina Kokawar Zuwa Turai


NIGER: KASUWAR BAJE KOLIN KAYAN KAMFANONIN MATASA
NIGER: KASUWAR BAJE KOLIN KAYAN KAMFANONIN MATASA

Tallafin ya kai nakudi CFA milyan ashirin.

Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Talemsi a jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijer ta taimakawa matasar jiha da kayan aiki da jari da ya kai miliyon ashirin da daya na CFA don kara musu kwarin gwiwa yin sana’a a gida.

Shugaban Kungiyar Talemsi mai zaman kanta yace kungiyar ta dauki wannan mataki ne ganin yanda matasa ke bin barauniyar hanya zuwa kasashen Turai wasu kuma suna bada kansu ga masu safarar bil adama, kana wannan taimako zai sa matasan su dogara ga sana’o’insu.

Shugaban na kungiyar yace an baiwa matasan zabi ne su nuna abubuwa da suke bukata da zasu yi sana’a da su. Bayan ya mika godaiya ga wadanda suka tallafawa wannan shiri ya yi kira ga matasan cewar a cikin gida aka basu wannan taimako don haka su yi amfani da kayan aikin a cikin gida.

Irin wannan taimako na cikin gudunmuwa da kungiyoyi masu zaman kansu a jamhuriyar Nijer ke yi ga yaki da safarar mutane. Sanusi Mahaman mamba ne kungiyar farar hula ya yi kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan taimako da Talemsi ta baiwa matasa.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG