Ngillari, Yace a Dage Zabe Sai Watan Afrilu-Saboda Batun Tsaro

Jihar Adamawa.

Gwamnan jihar Adamawa Bala james Ngillari yace dage zaben ya zama wajibi ganin yanayin da tsaro yake ciki a yankin arewa maso gabas.

Saboda dalilan tsaro a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, Gwamnan jihar Adamawa, Bala James Ngillari, ya bada shawarar a dage zaben zuwa watan hudu.

Yanzu haka, al’ummomin da hare-haren yan Boko Haram ya raba da gidajensu da sauran masu ruwa da tsaki,sun fara maida martani ga kalaman gwamnan jihar Adamawan, Mr. Bala James Ngillari, da yayi a wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar zabe ta yi da hukumomi daga jihohin Adamawa, Borno da Yobe, inda gwamnan Adamawan yayi kiran da a dage zaben dake tafe a watan gobe, har zuwa watan Afrilu.

Wasu daga cikin al’ummar jihar ta Adamawa sun maida martani cewa, gwamnan bada yawunsu yayi wannan kira na a dage zaben ba.

Shi dai gwamnan Adamawan,wanda yanzu haka mahaifarsa ta Madagali ke hannun mayakan Boko Haram, na cikin yan takara a zaben dake tafen,inda jam’iyarsa ta PDP ta bashi tikitin takarar kujerar majalisar dattawa.

Your browser doesn’t support HTML5

A Dage zabe zuwa Afrilu-Gwamna Ngillari