Shugaban Amurka Barack Obama ya soki jawabin da Firayin Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gabatar a gaban majalisun dokokin Amurka dangane da shawarwari kan shirin Nukiliyar Iran.
Yarjejeniyar da PM Isra'ilan ya ke adawa da ita na nuni da cewa idan har ta tabbata manyan kasashen duniya sun sallamawa Iran cewa ta ci gaba ta kera makaman nukiliya da zarar wa'adin ya cika.
Jawabin na Mr. Netanyahu ya janyo cece-kuce tsakanin manyan jam'iyun siyasar Amurka biyu, Demokrat da 'yan Republican idan wasu 'yan majalisun su ka kauracewa zaman hadin gwiwar.
Ko a Isra'ila kamar Amurka, jawabin ba kowa ne ya gamsu da shi ba.
Ana sa sharhin Farfessa Yusuf Alhassan na jami'ar Kansas ya ce Mr. Netanyahu bai sami biyan bukata ba.
Ya ce ai akwai 'yan Demokrat da ma Amurkawa da suke kallon jawabin da yadda aka gayyaci PM Isra'ilar, a matsayin renin wayo ko cin fuska ga shugaban Amurka Barack Obama.
Your browser doesn’t support HTML5