Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Dan Kungiyar ISIS Mai Sare Kawunan Mutane


Sarkin saran kungiyar ISIS Muhammad Emwazi
Sarkin saran kungiyar ISIS Muhammad Emwazi

Wasu kafofin labaru sun sanar cewa an bayyana sunan wanda kungiyar ISIS ke yin anfani dashi wurin sare kawunan mutane

Rahotanni da kafofin yada labarai suka bayar suna nuni da cewa an gano ko wanene dan kungiyar ISIS din nan wanda yake fitowa a faya-fayan bidiyo inda kungiyar take datse kawunan mutane da take garkuwa dasu.Sai dai hukumomin tsaro suna kashedi cewa a yi taka tsan tsan domin ta yiwu rahoton na bogi ne.

Rahotani sun ambaci abokan Mohammed Emwazi suna cewa shine dogon mutumin nan mai magana lafazin 'yan kasar Ingila da aka yiwa lakabin "Jihadi John" da turanci.

Wasu majiyoyi biyu daga gwamnatin Amurka sun gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun hakikance Emwazi ne mutumin da ya rufe fuskarsa a cikin faya fayan bidiyon da ISIS ta nuna inda aka daste kawunan mutane.

Amma wakilin Muryar Amurka a Rome, yace majiyoyi daga hukumomin tsaro a turai sunki su gaskanta ko su karyata labarin suna cewa "labarin yana da sarkakiya fiyeda yadda ake zato".

Wata kakakin majalisar tsaro ta Amurka tace har yanzu ana ci gaba da binciken Amurkawa da kungiyar ta kashe, duk da haka taki ta tabbatar da cewa "Jihadi John , shine Mohammed Emwazi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG