Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ga 'Yan Matan Birtaniya Uku da Suka Gudu a Istanbul Kasar Turkiya


'Yan matasan Britaniya uku akan hanyarsu ta zuwa shiga kungiyar ISIS
'Yan matasan Britaniya uku akan hanyarsu ta zuwa shiga kungiyar ISIS

Wani bidiyo ya nuna 'yan matana nan uku da suka bar Landan akan hanyarsu ta zuwa shiga kungiyar ISIS

‘Yan mata matasa guda uku ‘yan Britaniya da aka kyautata zaton sun yi balaguro zuwa Syria da nufin shiga kungiyar ISIS an gansu a wani bidiyon leken asiri a Turkiya.

Kafofin labaran kasar Turkiya sun ce hotunan sun nuna ‘yan matan suna shiga motar safa a Instanbul. Wannan shi ne karon farko da za’a ga ‘yan matan tun lokacin da suka bar Landan kusan makonni biyu ke nan.

Jami’ai sun ce basu da wani dalilin zaton kawo yanzu ‘yan matan suna cikin Turkiya. An kyautata zaton sun ketara ko zuwa cikin kasar Syria cikin yankin da ‘yan ta’adan ISIS suka mamaye.

‘Yan matan da suka fito daga arewacin Birnin Landan ajinsu daya. Su ne Shamima Begun ‘yar shekara 15 da Kadiza Sultana ‘yar shekara 16 sai kuma Amira Abase ita ma ‘yar shekara 15. Dukansu sun shiga jirgin kasar Turkiya ne zuwa Istanbul a tashar jiragen sama ta Gatwick dake cikin Birnin Landan ranar 17 watan jiya.

Bidiyon na mintuna biyu kacal ya nuna ‘yan matan uku suna fitowa daga ofisoshin motocin safa har na tsawon sa’o’i 17 ranar 17 ga watan Fabrariru zuwa 18 a yankin Esenler cikin Istanbul.

Jami’an tsaro sun ce akalla ‘yan Britaniya 500 suka bi Istanbul zuwa Syria domin shiga mayakan ISIS.

XS
SM
MD
LG