Wanda hakan nema yasa hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta yi kira ga kungiyoyin sa kai da kuma masu hannu da shuni da su taimakawa ‘yan gudun hijiran.
Tun farko hukumomin Kasar Kamaru suka ce za su maido da ‘yan Najeriya kusan dubu 12, to sai dai yanzu adadin wadanda aka maido sun kai kusan dubu 14 lamarin da ya sa jami’an hukumar ba da agaji ke ganin dole kungiyoyin masu zaman kansu shigo domin taimakawa.
Da yake taryar karin ‘yan gudun hijirar da aka maido na baya bayan nan babban jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, mai kula da sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar Adamawa Alhaji Sa’adu Bello, yace dole ne a hada hannu domin sake tsungunnar da ‘yan gudun hijirar.
Malam Aminu mai Kano Jami’in kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Red Cross, yayi bayanin taimakon da suke baiwa masu gudun hijirar inda yace kungiyar Red Cross na kula da wadanda suka zo a tagayyare da kuma cikin rashin lafiya, yanzu haka ma’aikatan kungiyar na shiga suna tambayar mutane, domin neman wanda ke bukatar kulawa.
Kamar yadda bayanai ke nunawa yawancin mutanen da ake maidowar ‘yan jihar Borno ne, wanda aka saka gwamnatin jihar turo da motocin da zasu ke kwashesu.
Saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5