Babban bankin ko CBN a cigaba da zagayawa jihohi ya shirya taron fadakarwa a Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo.
Taron na yini uku na fadakar da jama'a ne dake muamala da bankunan kasuwancin Najeriya.
Taron ya sami halartar kungiyoyin mata da na manoma da na 'yan kasuwa da na matasa da na dalibai da dai makamantansu.
Hajiya Khadijat Kasim mataimakiyar darakta a babban bankin ita ce ta jagoranci taron. Tace taron na gamin gambiza ne saboda akwai sassa daban daban da suke ta yawo suna fadakar da jama'a akan abubuwan da babban bankin ya kirkiro.
Taron na fadakar da jama'a ne akan mahimmancin daukan hoton tafin hannu saboda kare ajiyar da mutum ke da ita a banki da kuma shirin takaita daukan tsabar kudi kamar yadda 'yan kasuwa ke yi yanzu.
Kazalika bankin zai fadakar da jama'a akan shirin da ya yi na taimakawa masu karamin jari da kananan masana'antu akan yadda zasu iya samun lamuni da wurin da zasu je su samu. Zasu sani kuma cewa babban bankin ya kayyade kudin ruwan da zasu biya akan kowane lamuni aka basu saboda kada a kwaresu.
Babban bankin ya yiwa nakasassu kyakyawan shiri na samun jari musamman wadanda suke da aikin hannu.
Ga karin bayani.