Yankin Wukari dake kudancin jihar Taraba ya sha fama da tashe tashen hankula da sau tari kan rikide ya zama na kabilanci ko addini.
Yawan barkewar rigingimu ya sa yankin yanzu ya koma tamkar kufai. Yanzu din ma wani rikicin ne ya sake barkewa a yankin.
Wani ganao ya yiwa Muryar Amurka bayani akan abun da ya yi musabbabin haddasa rikicin baya bayan nan.
Wasu mutane ne suna dawowa daga kasuwa cikin motoci da suka kai shida sai kwasam a cikin daji wai Jukunawa suka bude masu wuta. Cikin motocin maharban sun kashe direban mota daya tare da mutane uku daga bisani kuma suka kone motar. Jukunawan basu kashe mata ba.
Inji ganao din har yanzu akwai gawarwaki cikin daji domin Jukunawa suna dajin da makamansu. Jami'an tsaro ne zasu iya shiga dajin su kwashe gawarwakin.
Amma shugaban hadakar kungiyar Jukunawa Mr Benjamin Bako ya musanta zargin da ake yi na cewa Jukunawa ne suka kai harin. Ya kara da bayyana irin kokarin da suke yi na samun zaman lafiya a yankin.
Mr. Bako yace ta yaya za'a tabbatar cewa Jukunawa ne suka kai harin alhali kuwa barayi sun yi yawa yanzu. Yace ko a hanyar Katsina Ala zuwa Takum an budewa wasu wuta an kuma kashe Jukunawa da yawa. Idan abu ya faru kamata ya yi a yi bincike a tabbatar da wadanda suka aiwatar da lamarin. Yace a daina dorawa Jukunawa laifin. Yace nasu kiran shi ne a kai zuciya nesa. Rikicin da suka sha yi bai taimakesu ba. Ya lalata kasar duka.
Rundunar 'yansandan jihar tace tana kokarin shawo kan lamarin tare da jan kunnuwan mutane da su mika makamansu ko kuma su gamu da fushin hukuma idan an kamasu. Shi ma gwamnan jihar ya yi tur da wannan sabon harin har ma ya kira taron masu ruwa da tsaki da zummar shawo kan matsalar.
Ga karin bayani.