Jami’in hukumar samar da agajin gaggawa ta NEMA, Mohammed Kanar ne ya shaidawa Muryar Amurka. Wanda kuma ya janyo hankulan jama’a da su mayar da hankali game da irin wannan tashin boma bomai da ke faruwa a unguwannin su.
“Yau da Asuba wadannan mutane sun sake kai wannan hari a wani masallaci a can unguwar Jiddari dake wata bayan kotu ta kwamitin tarayya, inda a can ne ma har wajen mutane 6 suka rasa rayukansu, yanzu kuma ‘daya ya karu suka zama bakwai, muna kuma da mutane wajen goma sha shida wanda har yanzu suna nan suna karbar magani.” Inji Mohammed Kanar jami’in hukumar samar da agajin gaggawa na hukumar NEMA.
A yau da missalin karfe biyar na safe ne dai aka sami tashin wannan bom din, a unguwar da ake kira Jiddari bayan High Court. Inda wani dan kunar bakin wake ya kutsa cikin wannan masallaci a dai dai lokacin da ake gudanar da sallar Asuba ya kuma tayar da bom din, da ya hallaka mutanen da raunata wasu da dama.
Irin wannan tashin bom a Masallatai dai ya zama tamkar ruwan dare, musammamma a unguwannin dake bayan gari inda irin wadannan mutane ‘yan kunar bakin wake kanyi jigida da boma bomai, su kuma kutsa ciki su tayar da su, su kashe kansu da kuma masallatan.
Saurari rahotan Haruna Dauda.