NDLEA: Hukumar Yaki da Fatauci da Sarafa Miyagun Kwayoyi Tayi Wawan Kamu

NDLEA

A wani taro na manema labarai da hukumar NDLEA ta kira a birnin Legas ta sanarda cafke wani mutumin da ya kware wajen sarafa muggan kwayoyi a jihar Anambra.

Mutumin dan shekaru talatin da bakwai sunasa Chukwuwendo Sylvester Ikeakor.

Ana ficewa da kwayoyin zuwa kasashen waje, irinsu Turkiya, China da Italiya. Ana biyan masu safaran zunzurutun kudi har dala dubu biyar kwatankwacin nera miliyan daya da dubu dari biyar.

Alhaji Ahmad Gyade shi ne shugaban hukumar ta NDLEA ya yiwa Muryar Amurka karin haske game da lamarin.

Yace mutumin na sarafa sabbin miyagun kwayoyi da yanzu ake yayinsu. Mutumin yana da mutanen dake yi masa aiki. Kowane aikin ana iya samun akalla kilo goma sha hudu. Kwayar a kasashen waje kudinta nada yawa.

Tuni hukumar tace ta gabatar da matashin a gaban kuliya bayan ta tabbatar da samun kwararan shaidu tare dashi da suka hada da manyan motoci na alfarma guda hudu da fili a Legas wanda kudinsa ya kai nera miliyan ashirin da biyar da gidaje na fiye da nera miliyan dari.

To saidai kuma duk da kokarin da hukumar keyi na hana masu fasa kaurin muggan kwayoyi a kasar, har yanzu ana samun 'yan kasar dake safara ko shan muggan kwayoyi.

Muryar Amurka ta tambayi shugaban hukumar ko baya ganin ya kamata su mayarda karfinsu akan fadakar da wayar da kawunan mutane. Sai yace yin hakan nada anfani matuka. Amma bisa ga nacewar mutane sun gano wani abu a bincikensu ya sa kome aka fada wasu ba zasu bari ba.

Yace wannan mutumin da suka kama cikin shekaru uku da ya fara sarafa kwayoyin yana da kudi samada nera miliyan dari uku a bankuna banda gidaje na fiye da nera miliyan dari da saba'in da biyar.

Ga rahoton Babangida Jibrin.

Your browser doesn’t support HTML5

NDLEA: Hukumar Yaki da Fatauci da Sarafa Muyagun Kwayoyi Tayi Wawan Kamu - 2' 54"