NBC Ta Ci Tarar TRUST TV Kan Wani Rahoto Da Ta Yada Kan Ayyukan Yan’ Ta’adda A Najeriya

Hukumar Kula da Kafofin Yada labarai ta Najeriya NBC

Hukumar da ke kula da kafafen yada labarai ta Najeriya NBC ta sanya wa kafar yada labarai ta TRUST TV da wasu kafafen guda hudu biyan tarar Naira miliyan biyar saboda gabatar da wani rahoton bidiyo na musamman kan ayyukan ’yan ta’adda a kasar.

ABUJA, NIGERIA - A cewar hukumar rohoton ya take ka’idoji da dokokinta kana ya na iya rura wutar matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Wannan mataki na hukumar NBC na zuwa ne kasa da mako daya bayan da Ministan yada labarai da al’adu a Najeriyar Alhaji Lai Mohammed, ya yi barazanar cewa gwamnatin kasar za ta hukunta kafafen da aka samu da gabatar da rahoton bidiyo na musamman kan ayyukan ‘yan ta’adda a kasar bayan zargin cewar hakan tamkar taimaka wa ‘yan’taddan ake yi.

Sai ga shi jiya Laraba hukumar ta fitar da wata wasika da ta bayyana sunanyen wasu kafafen yada labarai da aka ci tararsu Naira miliyan biyar ciki har da kafar Talebijin ta TRUST TV.

Malam Balarabe Shehu Illela, wanda shi ne shugaban hukumar ta NBC a Najeriya, ya shaida wa Muryar Amurka dalilan da su ka sa aka kai ga daukar wannan matakin, kamar yadda za a ji a sautin cikakken rahoton.

A ranar biyar ga watan Maris din wannan shekara ta 2022 ne kafar talabijin din TRUST TV a Najeriya ta saki wani rahoton bidiyo na musamman kan ayyukan ‘yan ta’adda a kasar. Bidiyon dai na dauke da rahotanni na hakika daga ‘yan bindiga, masana da kwararru a bangaren tsaro da kuma mutanen da harin ‘yan bindiga ya shafa, kamar yadda shugaban gidan telebijin din, Ibrahim Shehu Adamu, ya bayyana.

Tuni dai masu ruwa da tsaki a kasar suka shiga tofa albarcin bakinsu kan wannan hukuncin

Kazalika hukumar NBC ta ce za ta sanya takunkumi ga kafar yada labarai ta BBC bisa wani shirinta na binciken kwakwaf kan ayyukan ta’addanci da barnar ‘yan bindiga a Najeriya.

Matsalar tsaro a Najeriya dai na neman kai wankin hula dare, inda ‘yan kasar ke ci gaba da zaman dardar.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

NBC Ta Ci Tarar TRUST TV Kan Wani Rahoto Da Ta Watsa Kan Ayyukan Yan’ta’adda A Najeriya.mp3