Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Wata Barazana Daga ‘Yan Ta’adda 'Yan Sandan Najeriya Sun Karfafa Tsaro A Abuja


Bayan Wata Barazana Daga ‘Yan Ta’adda 'Yan Sandan Najeriya Sun Karfafa Tsaro A Abuja Tare Da Karin Ma'aikata
Bayan Wata Barazana Daga ‘Yan Ta’adda 'Yan Sandan Najeriya Sun Karfafa Tsaro A Abuja Tare Da Karin Ma'aikata

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tura karin ma’aikata a kusa da Abuja domin karfafa tsaron “muhimman kadarorin kasa da kuma wurare masu bukatar karin kulawa,” in ji kakakinta a yau Talata, 'yan kwanaki bayan rahotannin wani hari a wani shingen bincike da ke kusa da babban birnin.

WASHINGTON, D. C. - Kasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afirka na fuskantar matsalar rashin tsaro daga masu tayar da kayar baya a yankin arewa maso gabas, da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa a arewa maso yammacin kasar da kuma wasu kungiyoyin masu aikata laifuka da ke yawo a kasar.

‘Yan Sandan Najeriya
‘Yan Sandan Najeriya

Jaridun kasar sun ruwaito a ranar Alhamis din da ta gabata cewa wasu da ake zargin mayakan wata kungiya mai da'awar kishin Islama ne suka kai hari a wani shingen binciken sojoji a wani yanki da ke kan iyakar Abuja da jihar Neja, inda suka kashe wasu sojoji.

Sojojin Najeriya da 'yan sandan kasar ba su amsa bukatar jin ta bakinsu kan harin da aka ruwaito ba.

'Yan Sandan Najeriya
'Yan Sandan Najeriya

Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) na kasa, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Sufeto Janar Usman Alkali Baba ya kawar da fargabar mazauna yankin dangane da “barazanar tsaro da ake gani a baya-bayan nan,” wanda bai yi cikakken bayani ba.

Adejobi ya ce NPF tana tura “karin jami’an ‘yan sanda da kadarorin aiki a cikin babban birnin tarayya da kewaye domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mazauna ciki, muhimman kadarorin kasa da kuma wurare masu rauni.

Najeriya na da ‘yan sanda sama da 350,000, wanda masu sharhi kan harkokin tsaro ke ganin bai isa ba wajen samar da ingantaccen tsaro a kasar da ke da mutane sama da miliyan 200.

-REUTERS

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG