Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun shugabanta, Emmanuel Osodeke, inda ta bayyana rashin cika alkawuran da gwamnatin Najeriya ta yi da kuma yin watsi da kiran.
Sanarwar da shugaban kungiyar, Emmanuel Osodeke ya sanya wa hannu, ta ce an dauki matakin ne yayin wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kasa a ranar Lahadin da ta gabata a hedikwatarta da ke harabar jami’ar Abuja.
ASUU ta ce taron gaggawa na NEC ya zama wajibi tun bayan da ta fito fili ta sanar da tsawaita yajin aikin na tsawon makonni 12 a watan Mayu.
Ta ce gwamnatin Najeriya ba ta nuna himma wajen ganin an shawo kan rikicin da ya kunno kai ba, ta kuma ce za a kara wa’adin makonni hudu don sa ido kan yadda gwamnatin ke da niyyar magance matsalolinta.
Sanarwar ta ce; “Bayan tattaunawa mai zurfi tare da fahimtar gazawar gwamnati a baya wajen cika alkawuranta wajen magance matsalolin da suka taso a cikin yarjejeniyar FGN/ASUU ta 2020 (MOA), NEC ta yanke shawarar kare wa'adin yajin aikin zuwa wasu makonni hudu domin bai wa gwamnati karin lokaci don gamsuwa da warware dukkan batutuwan da suka rage”.
A ranar 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta ayyana yajin aikin a fadin kasar saboda matsalolin rashin walwala, rashin sake tattaunawa a kan wasu yarjejeniyoyin da suka rattaba hannu a baya da kuma zargin gwamnati na sanya tsarin albashi na IPPIS.
Sakamakon abin da ta kira gazawar gwamnati na yin kasa biyan bukatunta, kungiyoyin sun ci gaba da ba da sanarwar tsawaita ayyukan masana'antu, tare da dakile ayyukan ilimi a cikin jami'o'in gwamnati na kasar.
A halin da ake ciki, takwarorin nata da ba na ilimi ba su ma tun daga lokacin suka fara yajin aiki makamancin haka, wanda ya haifar da durkushewar tsarin jami'o'in gwamnati gaba daya a Najeriya.