Nazarin Kwararru Da Masana Kan Dabarun Yaki Da Ta’addanci A Yankin Sahel

Yaki Da Ta'addanci a Yankin Sahel

Kwararru da masana daga Afirka ta yamma sun gudanar da wani nazarin sabbin dabarun tunkarar aiyukan ta'addanci da ke kara ta'azzara a yankin a halin yanzu.

Kwararru da masana daga kasashen Togo da Mali da Mauritanie da kuma wakili daga Chadi, sun share kwanaki biyu suna nazarin hanyoyin dakile yaduwar ta'addanci da ma cike gibin da ya haifar da karuwar annobar a cikin kasashen yankin sahel.

Sakamakon aiyukan ta’addanci dake kara ruruwa a yankin sahel, ya sa masana da kwararru kan sha’anin tsaro gudanar da taron kwanaki biyu a Agadas, inda su ka yi nazarin sababbin dubarun hada kai da nufin tunkarar annobar.

Bazuwar kananan makamai da tsananin talauci da rashin mulki na gari na taimakawa wajen bazuwar ta’addanci a yankin a cewar wedrago coulibaly, masanin harakokin tsaro a kasar mali.

Ya ce yaki da ta’addanci na bukatar kallon tsaf dole ne shugabannin kasashen yankin su warware ginshikin ta’addanci, kamar talauci da wariya da kuma adalci to sai dai kuma hakan baya nufin maganar baki kawai, dole ne sai kasashen sun hadu tare da yin aiki tare.

Kamar yadda masana ke cewa akwai bukatar tunkarar annobar talauci da kuma tabbatar da adalci kan kowa, sai dai sauyi a guguwar siyasa a yankin sahel zai yi tasiri sosai acikin yakin, a cewar Conde Sekou kwararre kan sha’anin tsaro a kasar Togo.

Ya ce sakamakon sauye sauyen da ake samu a yankin sahel game da batun shugabanci barazana ne ga inganci na dubarun yaki da ta’addanci, kuma ana bukatar kallon sabon kalubalen nan take da nufin nazarin irin mataki na gaba domin a taimakawa wannan fanni.

Domin karin bayani saurari rahotan Hamid Mahmud.

Your browser doesn’t support HTML5

Nazarin Kwararru Da Masana Kan Dabarun Yaki Da Ta’addanci A Yankin Sahel - 2'02"