WASHINGTON, D. C. - Shugaban kasar a ranar Laraba ya ce za a gudanar da harkonin wannan rana ta wajen ayyukan dashen itatuwa na kasa don taimakawa wajen dakile illolin sauyin yanayi. Ambaliyar ruwa ta mamaye Kenya tare da wasu sassan gabashin Afirka inda fiye da mutane 235,000 suka rasa matsugunansu kuma suna zaune a sansanoni da dama.
Shugaba Ruto ya kuma sanar da sake bude makarantu a duk fadin kasar, bayan jinkirin makonni biyu sakamakon mamakon ruwan sama da ya lalata daruruwan makarantu.
Gwamnati ta ce sama da makarantu 1,000 ne ruwan sama da ambaliyar ruwa ta shafa tare da ware kudade don gyarawa.
Sashen nazarin yanayi a hasashen yanayi da ya ke yi na yau da kullun ya ci gaba da yin hasashe kama daga matsakaici ruwan sama zuwa mamakon ruwan sama a mafi yawan sassan kasar.
Gwamnati na shirin kwashe mutane ala daga yankunan da ke fama da ambaliya da kuma wadanda ke kusa da koguna da madatsun ruwa yayin da yawan ruwa a cikin manyan madatsun ruwa na kasar ya yi karuwa mai kafa tarihi.
A wannan makon, gwamnati ta rushe gidaje a matsugunan Mathare da Mukuru na Nairobi babban birnin kasar kuma shugaban kasa ya yi alkawarin bai wa iyalan da aka kora kwatankwacin dalar Amurka 75 don sauya matsuguni bayan wa'adin da aka ba su na kwashe yayin da ake tafka ruwa mai hadari.
-AP
Dandalin Mu Tattauna