Nakasassun Jihar Yobe Suna Korafi Gwamnat Tayi Watsi da Su

Wasu nakasassu.

Gamayyar nakasassun jihar Yobe tace gwamnati ta kasa cika alkawarin da tayi na basu kashi ashirin cikin kason kudin raran man fetur da take samu daga gwamnatin tarayya.
Alkawrin da gwamnatin Yobe ta yiwa kungiyar nakasassun jihar na samar masu da kashi ashirin cikin abun da jihar ke samu daga raran kudin man fetur domin inganta rayukarsu bata cika ba.

Shugaban kungiyar gamayyar nakasassun Muhammed Abba Musa yace su a jihar Yobe sun yi watsi da duk wani umurnin da aka basu domin basu ga anfanin rarar kudin man fetur din ba. Duk da wai gwamnatin tarayya tace a ba nakasassu kashi ashirin na kudin a kowace jiha ke samu daga rarar man fetur, su a Yobe lamarin ba haka yake ba. Yace idan da za'a iya bayar da kashin zai taimaka wurin dauke ma nakasassun wahalolinsu.

Kason nasu zai iya kai ga basu damar yin karatu, su koyi wasu ayyuka ko sana'o'i da zasu iya dogara da kansu ba tare da yin bara ba. Sauran jihohi da yawa an basu kashi ashirin din amma ban da jihar Yobe.

Wuraren da aka kafa domin koyawa makafi sana'o'i an barsu ba'a gyara ba duk da cewa gwamnatin tarayya ta bayar da kudi a gyarasu. Idan da za'a gyara wuraren koyon ayyukan da an taimakawa nakasassu.

Daga bisani sun kira gwamnan jihar Ibrahim Geidam da ya taimakawa nakasassun jihar Yobe domin suna cikin halin kuncin rayuwa idan da can bai sani ba.

Mai ba gwamnan shawara akan harkokin nakasassu Alhaji Ibrahim Bukar Gonori yace duk abubuwan da suka shafi nakasassu sun rubuta sun ba sakataren gwamnati Baba Gwani Macina. Yace babu shakka abubuwan da suka rubuta zasu isa gaban gwamna sabili da haka suna rokonsa ya share masu hawaye domin su ma su ji dadi kamar yadda wasu ke ji.

Ga rahoton Sa'adatu Fawu.

Your browser doesn’t support HTML5

Nakasassun Jihar Yobe Suna Korafi Gwamnati Tayi Watsi da Su - 3'25"