Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darikar Tijjaniya ta Kaddamar da Gidauniya


Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Darikar Tijjaniya ta kaddamar da gidauniya a Abuja ta nera biliyan daya da miliyan dari tari domin inganta ilimin addinin Musulunci da na boko.

A dakin taro na kasa da kasa dake Abuja babban birnin Najeriya 'yan darikar Tijjaniya sun yi taron kaddamar da gidauniyar inganta ilimin addinin Musulunci da na boko.

Gidauniyar ta nera biliyan daya da miliyan dari tara za'a yi anfani da kudaden ne a gina cibiyar Muslunci a Abuja. Shugaban Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne uban gidauniyar. Ya dauki lokaci yana kokawa ga abun da yace suna raba kan Musulmi.

Shettima Rijiya Faruk Gusau shi ma dan Tijjaniya ya halarci taron. Yace ya ga mutane daban daban a wurin taron wadanda suka bada gudunmowa. Yace da kadan kadan za'a cika gidauniyar har ma a wuce abun da ake bukata. Yace haraka ce ta Ubangiji kuma shi yake tanada abubuwansa.

A wurin taron kudaden da aka tara sun kasa nera miliyan dari. Amma Faruk Gusau yace idan an bi shehunnai da sauran malaman zasu iya hada kudin. To saidai mutane da dama sun yi alkawura

Gidauniyar tana karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III da kuma mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo. Gidauniyar ta samu halartar kakakin majalisan wakilan Najeriya Aminu Tambuwal da gwamnan Kaduna Ramalan Yero.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG