Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masarautar Minna ta Kadu da Rasuwar Sanata Dahiru Kuta


Sanata Dahiru Awaisu Kuta wanda Allah Ya yiwa rasuwa jiya a Legas.
Sanata Dahiru Awaisu Kuta wanda Allah Ya yiwa rasuwa jiya a Legas.

Rasuwar Sanata Dahiru Awaisu Kuta ta jefa masarautar Minna cikin wani halin juyayi da bakin ciki

Masauratar Minna a jihar Neja tace ta kadu da mutuwar Sanata Dahiru Awaisu Kuta wanda Allah ya karbi ransa jiya a wani asibiti a Legas.

Masarautar tana daya daga cikin masarautu uku dake cikin yankin da marigayin yake wakilta a majalisar dattawan Najeriya. Alhaji Usman Nagogo Ciroman Minna yace mai martaba sarkin Minna da duk ilahirin masarautar suna cikin alhini da juyayi sabili da rashin sanatan. A majalisar dattawan Najeriya ya tsaya masu, tsayuwa ta hakika har ma ana shirin yi masu wata wutar lantarki. Tun daga lokacin da aka bayyana shirin wutar lantarkin yake shiga yana fita ya ga yadda za'a gudanar da aikin.

Tuni dai gwamnatin jihar Neja ta fitar da sanarwar nuna juyayi game da mutuwar Sanata Dahiru Awaisu Kuta. Alhaji Tanko Dada babban daraktan hulda da jama'a a gwamnatin jihar yace sun yi bakin ciki da rashin da ya samesu domin sanatan yayi aiki matuka a rayuwarsa. Ya yiwa gwamnatin jiha aiki. Ya yiwa ta tarayya ma.

Sanata Nuhu Aliyu da yayi aiki da marigayin yace an samu gurbi mai wuyar cikawa a siyasance.Yace duk cikin wadanda suka fito babu irinsa.

Da can an sha raderadin rasuwarsa inda ma yace duk wanda yana ganin ba zai mutu ba mutumin banza ne. Yace Allah nada ikon daukar ransa duk lokacin da Ya ga dama. Idan mutum bashi da lafiya ya nemi magani.

Masarautar ta dage yin jana'izarsa zuwa karfe goma na safiyar yau.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG