WASHINGTON, DC —
Sashen Hausa na Muryar Amurka tare da Kungiyar Muryar Talakawa sun shirya taron ilimantar da fadakar da jama'a.
Ranar Larabar da ta gabata suka yi taron farko a birnin Kano kafin su yi wani a Gusau a karshen mako.
Manufar tarukan ita ce ilimantarwa tare da fadakar da jama'a dangane da wannan tasha ko kuma kafar sadarwa ta Dandalinvoa.com da kuma neman bayanai da shawarwari daga masu saurare akan yadda yakamata tashar ta rinka gudanar da ayyukanta domin dacewa da bukatun al'ummar wannan zamani
Malam Ibrahim Alfa Ahmed babban edita mai kula dandalin yayi bayani. Yace dandalin voa kamar yadda aka sani "sabuwar kafa ce ta yada labarai da ake iya kamata a wayoyi na mobile da kuma irin kwamputa din nan na hannu wato handa held ke nan" Ya ci gaba da cewa "ganin yadda irin wadannan abubuwa suka bunkasa cikin wannan zamanin kuma ganin cewa yanzu yadda labarai suke yaduwa cikin sauri ya kamata a samu kamar wata kafa wadda zata rika bada labari mai sahihanci ga duniya da zara abu ya faru ba wai kawai a ji ta kan Facebook ko ta Twitter ba ko ba gaskiya ko da gaskiya" dalili ke nan aka kafa dandalin voa.
Bayanan da suka tattara a wurin tarukan Ibrahim Alfa yace zasu yi anfani da su wurin yin nazari akan irin abubuwa da jama'a ke so. Idan an zo tsara takamanmun shirye-shirye za'a yi la'akari da ra'ayoyin da jama'a suka bayar.
Bala Kofar Sabuwa shugaban kungiyar Muryar Talaka na kasa baki daya yace sun yi farin ciki tun ranar da aka kafa tashar dandalinvoa musamman domin tashar tana bude sa'o'i ashirin da hudu kowace rana. Yace kowane lokaci ana iya budeta a samu labaru da dumi-duminsu. Yace sun yi murna da yadda Muryar Amurka take kawo masu abubuwa dake tafiya da zamani.
Ga cikakken bayani.