A baya makafi da masu matsalar gani na amfani da littattafan makafi wajen koyan ilimi a kasar Kenya, amma yanzu haka makarantun sun fara amfani da wata sabuwar fasahar zamani, wadda ke fitar da magana mai makon rubutu.
Wani matashi mai shekaru 17 yanzu haka yana bincike kan yanar gizo don samun bayanai. Yanzu haka dai wannan dalibin koyon ilimin halitta, duk da yake makaho ne kuma a shekaru biyu da suka wuce yayi ta kokarin zuwa koyan ilimin komfuta a wata makatarantar makafi.
Idan aka duba littattafai irin na makafi na da matukar tsada, amma kasancewar wannan fasaha da aka samu ta kawo sauki ga masu wannan nakasa, idan aka duba yadda zasu iya amfani da kwamfuta wajen binciken duk abinda suke bukata, ba tare da sun kashe kudinsu ba wajen sayen littattafai masu tsada.
Makarantu sun fara amfani da wannan fasaha ne shekaru shida da suka gabata, wadda yake baiwa ‘dalibai makafi damar shiga yanar gizo ta kwamfutar su ko ta karamar na’urar nan ta Ipad.
Yanzu haka cikin makarantun makafi 11, makarantu 4 sun fara amfani da fasahar, haka kuma kungiyar InAble tace zata taimaka wajen biyawa sauran makarantun suma su fara amfani da fasahar.