Karuwar yawan wadanda suke zuwa umrar Ramadan na faruwa ne saboda dimbin ladan dake tattare da wannan ibada a cikin Ramadan kamar yadda malamai ke fadi.
Saidai umrar Ramadan ta bana ta zo da kalubalen karanci da kuma tsadar kujerun zuwa wannann umrar lamarin da wasu ke dora alhakin kan kamfanonin dake shirya tafiye-tafiyen umrar.
Alhaji Umaru Labaran Dangadi shugaban kamfanin Umariya Travels and Tours yace ya san a Saudiya lokacin Umra otel ke tsada da mota wadanda suka sa biza ta yi tsada ita ma. Yace otel din dake daukan mutane dari biyar amma sai a bada biza kasa da dari biyu. Saboda haka otel din dole ne ya ninka kudin mutane dari biyar akan dari biyu. Haka ma kamfanonin motoci su ke yi. Abun da ya sa biza take tsada ke nan a Najeriya amma ba wai kamfanonin shirya tafiye-tafiye sun bushi iska su kara kudi ba ne.
Alhaji Labaran ya cigaba da cewa akwai kamfanonin dake da adadin mutum dubu hudu da, da azumi amma yanzu ba zasu sami bizan mutane fiye da dari uku ba. Yace kafin azumi ana basu biza akan dala dari biyar amma da azumi ya zo an mayar da biza dala dubu daya da dari biyar daga Saudiya.
Malamai sun ja hankalin mutanen da suka so tafiya umrar bana amma basu samu sukunin yin hakan ba. Dr Bashir Aliyu Umar limamin masallacin Juma'a na Alfurkan dake Nasarawa GRA a Kano yace yayinda mutum ya yi niyya zuwa umra amma kuma wani abu ya taso bai iya zuwa ba to ya yi kokari ya yi anfani da dukiyar da Allah ya bashi da zai yi umra da ita to ya taimakawa wadanda ke fama da tsananin rayuwa. Allah zai bashi dimbin ladar zuwa Umra. Jin tausayin bayin Allah zai ba mutum rahamar Allah.
Ga karin bayani daga Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5