Amirul Hajj na Najeriya kuma Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Elkanemi, shi ya bayyana wannan a wurin wani taron da shugabanni da dukkan masu ruwa da tsaki a ayyukan Hajjin na bana suka shirya a Jeddah.
Shi kuma shugaban hukumar alhazai ta Najeriya, Alhaji Musa Bello, yace za su mayarda hankalinsu bana kan batun tsabta a tantunan Mina da Arafat, domin kawar da irin abubuwan da ake gani na rashin tsabta. Yace za a tabbatar da samun hanyar wucewar ruwan alwala ko kwashe tarkaccen abinci daga tantunan alhazan.
Za a kafa kwamitin tsabtan da zai kula da hakan.
Haka kuma hukumomin Sa'udiyya sun tsara kwasar alhazai daki-daki zuwa Mina da Arafat domin kaucewa cunkoso. Za a kwashi alhazan Najeriya zuwa wadannan wurare biyu daga karfe 12 na daren lahadi.
Wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari, ya aiko da karin bayani daga Makkah.