Sarkin Musulmin ya kuma roki alhazai masu karfin jiki da zasu yi aikin Hajjin bana, da su zamo masu taimakawa sauran alhazai marasa karfi, kamar tsoffi da mata da yara. Yace hakki ne a wuyarsu, su kula da sauran 'yan'uwansu alhazai.
Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar, yace idan Allah Ya nuna mana shekara mai zuwa, zai mika wannan wakilci na Amirul Hajj ga wani daga bangaren kudancin kasar.
A bana dai, hukumomin Sa'udiyya sun rage yawan alhazai a fadin duniya da kimanin kashi 20 cikin 100, a saboda manya-manyan ayyukan da ake gudanarwa na fadada wuraren yin ibada a Kasa Mai Tsarki. Idan aka gama wadannan ayyukan, hukumomi sun ce alhazai zasu samu saukin gudanar da ayyukansu na ibada a lokacin Hajji da na Umrah.
Ga rahoton Nasiru Adamu el-Hikaya daga Abuja kan wannan batun.