Hukumar Kwastan din Najeriya ta ce kasar ta rufe bakin iyakarta da jamhuriyar Benin domin kasar ta karya dokar kasa da kasa lamarin da ya hana kaya shigowa kasar daga Benin.
WASHINGTON, DC —
Kawo yanzu sama da watanni biyu ke nan da kayayyaki suka daina shigowa daga Jamhuriyar Benin zuwa cikin Najeriya.
Hana kaya shigowa cikin Najeriya ya biyo bayan abun da hukumar kwastan Najeriya ta ce karya dokar kasa da kasa da ita jamhuriyar Benin ke yi. Alhaji Abdullahi Dikko Nde shugaban kwastan na Najeriya shi ya sanarda manema labarai a birnin Legas. Shugaban ya ce ba zata yiwu ba kasashen biyu su sa doka amma daya daga cikinsu ta noke tana yin yadda ta ga dama. Ya ce muddin jam'an kwastan din jamhuriyar Benin basu bi doka ba kamar yadda aka shata to ko bakin iyakar kasashen biyu haka zai cigaba da zama a rufe kuma babu wani kaya da za'a bari ya shigo.
A cikin bayaninsa Alhaji Nde ya ce abun da doka ta tanada shi ne idan kaya ya shigo kan hanyarsu zuwa Najeriya to dan Benin kada ya karbi sisin kwabo na dan Najeriya. Abun da zai yi kawai shi ne ya tattara kayan ya kawo ma kwastan. To amma 'yan Benin basa yin haka. Sai su bari kaya suna shigowa yadda suka ga dama. Basu tsaya nan ba suna buge ofisoshinsu suna kuma kashe jami'an kwastan din Najeriya. Ya ce dalili ke nan da ya hana. Ya ce idan sun bi ka'ida suma zasu bi ka'ida. Ya ce ya gayawa minista da shugaban kasa a tafi a yi taro a Benin. Idan basu ji ba to a rufe iyakar gaba daya.
Dangane da ko hakan kamar ana yiwa kasar Benin bita da kuli ne sai ya ce shi ba zai bari a cigaba da kashe masu jami'ai ba.Jamhuriyar Benin ce ke bita da kuli domin ta ki bin ka'ida. Ya ce a duk duniya haka ake yi. Ya ce me ya sa basa yiwa kasashen Togo da Ghana hakan.
To sai dai wasu 'yan kasuwa sun koka da yadda wasu 'yan kwastan ke kwace masu kaya da hukumar ta sake ko su tsare kayan na lokaci mai tsawo wai sai sun biya harajin da ya kamata su biya. Amma ya ce sun baiwa 'yan kasuwa lambobi uku kuma wadanda suke rike dasu basa barci. Ya ce duk wani dan kwastan da ya kama kayan du suka riga suka saki to zai yi bankwana da aikinsa. Sai sun koreshi, kana su nunashi a kafar telibijan cewa shi ne dan hana ruwa gudu.
Ladan Ibrahim Ayawa nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5