Sai dai hare-haren sun barnata hanyoyi masu tazarar kilomita masu yawa a tsakanin sansanin sojin jiragen saman Nigeria da kuma barikin bataliyar rundunar soja ta 33. Anga matasa da kananan yara sun yi cincirindo a kewaye da konannun gawarwakin wadaanda ake zargin ta masu kai hare-haren ne a kan kekuna.Sannan wanda yaga abinda ya faru da idonsa ya nuna gawa da yatsansa yana cewa kunga Dan Boko haram ne dake dauke da bindiga a hannunsa- hadin gwiwar soja da mutanen gari suka kama sannan suka harbe shi, amma suka kawo gawarsa nan suke jefar amma suka cinna wuta a gawar domin konata.
Wani abin mamakin shine yadda mutane ke taruwa suna kallon yadda ake konar gawar. Gefe daya kuma mazauna inda ake konar gawar suka rika nunawa da yatsunsu konanniyar motar da duk jikinta tabon harbe-haren bindigogi ne. ‘Yan kallon kuma suka rika nunawa ‘yan jarida gawarwakin mazauna wurin biyu da suka ce harbesu aka yi suka mutu har lahira, kuma an harbesu ne a kansu.