Zaman sulhun da bangarorin biyu suka yi ya samu shiga tsakani na shugaban karamar hukumar Ethiope da wakilan bangarorin biyu, wato Fulani da 'yan kasar. Bangarorin sun bayyana korafe-korafensu. Mr. Ishyaku Iwu ya ce yawancin lokuta Fulani suna ratsawa kauyukansu da bindigogi suna yi masu barazana tare da cin zarafin matansu har da yi masu fyade. Hakan ba kyau kuma sam bai dace ba. Amma kuma tun da magana ce ta sulhu suna fata za'a samu sauki.Alhaji Lawal Ihoroje cewa ya yi Fulani suna shiga gonakansu suna cinye masu shuki su yi masu barna. Bayan haka sai su shanye ruwan da suka ajiye a jarka kana su sassare jarkokin.
A bangaren Fulani Alhaji Maikudin Ningi shugaban kungiyar Miyetti Allah ta jihar Delta ya ce dama ya dauki alkawari ya bi kowace karamar hukuma ya jawa Fulani kunne da su zauna lafiya da manoma. Ya ce to gashi an fara domin sun fi sati uku da fara irin wannan zaman. Da yaddar Allah wannan shi ne hanyar cin nasararsu a jihar Delta. Shi kuma Sha'aibu Haruna Sogidi shugaban matasan Fulanin Najeriya ya ce yarjejeniyar zaman lafiyar ta tanadi cewa idan an taba shanu su zasu nemi wanda ya taba shanun domin basu da shanu. Idan kuma an yi masu barna a gona wajibi ne Fulani su gano wanda ya yi masu barna sabo da zaman lafiya.
Mr. E. O. Sunday shugaban rikon karamar hukumar Ethiope wanda ya shirya taron sulhun ya ce a taron da suka yi tsakanin Fulani da kungiyoyin manoma da alamun samun sauki domin an kaiga zaman lafiya. Ya ce sun saurari kowane bangare kuma sun samu hadin kansu abun da zai kaiga yafewa juna lamarin da zai kawo karshen rikice-rikicen da ake samu tsakanin Fulani da manoma.
A nata bangaren rundunar 'yansandan jihar Delta ta yi marhaban da wannan sulhun kamar yadda kwamishanan 'yansandan Okechukwu Aduba ya shaidawa wakilin Muryar Amurka.
Lamido Abubakar Sokoto nada karin bayani.