Da ya ke jawabi a wurin taron tattalin arzikin yankin arewa maso gabashin Nijeriya da aka yi a garin Gombe, shugaban na Nijeriya ya ce ba za a bar arewa maso gabashin Nijeriya a baya ba a batun samar da damar cigaba. Ya ce shi fa bai ma yadda cewa talauci ne musabbabin tashin hankali a arewa maso gabashin Nijeriya ba. Ya kuma ce gwamnatin tarayya ba za ta hana ma arewa maso gabashin Nijeriya duk wani abin kawo cigaba ba. Hasalima, in ji shi, gwamnati za ta tashi haikan wajen ganin cewa yankin ya kubuta daga matsalar tsaro da kuma tattalin arziki.
Shi kuwa mai masaukin baki gwamnan Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dan Kwambo godewa ya yi ma Shugaban kasar saboda zuwa da ya yi ya bude taron. Ya ce wannan ya karfafa masu gwiwa sosai.
Wani sanannen dan siysar yankin kuma tsohon dan Majalisar Dattawa Salisu Ibrahim Musa Matori cewa ya yi an sha tarurruka irin wannan ba tare da an aiwatar da abin da taron ya cimma ba. Don haka ya yi kira ga wadanda alhakin abin ya rataya a wuyansu da su tabbatar an aiwatar da kudurorin bayan taron.