Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayyukan Noma da Ilimi Su Ne Zasu Habbaka Tattalin Arziki


Gombe, Najeriya
Gombe, Najeriya

A taron tattalin arzikin jihohin arewa maso gabas na kwana daya da aka yi a Gombe masana sun yadda cewa mayarda hankali kan ayyukan noma da ilimi su ne zasu habbaka tatalin arzikin yankin.

Shugaba Goodluck Jonathan ya bude taron habbaka tattalin arziki na kasa na shiyar arewa maso gabas da aka yi a Gombe. Taron shi ne irinsa na biyu.

Taron ya mayar da hankali ne kan ayyukan noma da ilimi da samar ma matasa aikin yi wadanda aka ce su ne zasu magance rikicin da shiyar ke ciki su kuma habbaka tattalin arzikinta. Taron ya samu halartar gwamnoni da kwararru daga shiyar da ma wasu wurare.

Kodayake babu wani sabon albishir da ya fito daga jawabin shugaban kasar masana sun ce ya zama wajibi gwamnonin shiyar su mayar da hankali kan ayyukan noma da ilimi da samar da ayyukan yi ga matasa wadanda 'yan ta'ada kan jawosu shiga ayyukan ta'asa. Ta haka ne kawai yankin zai fita daga kangin talauci da rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki.

Tsohon ministan tsare-tsare na gwamnatin tarayya Dr Shamsudeen Usman na cikin wadanda suka bada kasidu a wurin taron inda ya yi hannunka mai sanda ga 'yan siyasa. Ya ce dole ne a dauki matakan kawar da rashin aikin yi da rashin ilimi da jahilci. Abun da yake cinna ma matsalolin wuta su ne 'yan siyasa wadanda suke tara yara suna basu kawaya kana su tafi da su wajen siyasa domin a yi anfani da su. Ya ce 'yan siyasa su yi hankali. Kunna wuta da suke yi lokacin da ta zama gobara zata dawo ta hada da su. Ya ce yanzu abun da ake ciki ke nan a arewa.

Shi kuma Dr Bala Mohammed ministan birnin tarayya wato Abuja ya ce hanyar fita daga kangin da shiyar ta shiga shi ne kawo tattalin arziki da kawo ma'adanai da kawo sufuri da tsarin gyara duk abubuwan da suka tabarbare daya bayan daya domin a magancesu.

Dangane da taron farko Dr Bala Mohammed ya ce basu ji dadi ba domin babu abun da ya biyo bayan taron na cigaba. Amma wannan taron na biyu zai zama kaman na bude ido domin wannan taron ne ya tara duk 'ya'yan shiyar arewa maso gabas su kawo nasu hupbasan. Taron farko tamkar taron sahan shayi ne bayan haka kuma aka watse. Yana fata wannan taron zai sha ban-ban domin shugaban kasa ya ce a duba mene gwamnatin tarayya zata yi? Menene na jihohi zasu yi da na kananan hukumomi? Duk a fito da su kada a barsu kawai suna biyan albashi kowane wata.

A nashi jawabin shugaban gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Neja Dr Babangida Aliyu ya ce akwai bukatar shugabanni su kamanta adalci. Ya ce idan gwamnoni suka yi aiki bisa ga rantsuwar da suka dauka kafin su kama aiki to lallai za'a samu cigaba. Amma idan shugabanni suka yiwa adalci rikon sakainar kashi to abubuwa zasu kara tabarbarewa.

Ga rahoton Sa'a datu Fawu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG