Najeriya Ta Koma Matsayi Na 36 A Iya Taka Leda A Duniya

Super Eagles (Hoto: Facebook/Super Eagles)

Kungiyar ta Najeriya, wacce ta lashe kofin Afirka sau uku, tana matsayi na 39 a duniya a baya.

Super Eagles ta Najeriya ta haura matsayi uku a sabon jadawalin kungiyoyin kwallon kafa na maza da Hukumar Kwallon ƘKafa ta Duniya (FIFA) ta fitar.

FIFA ta fitar da sabon jadawalin kungiyoyin maza a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis.

Kungiyar ta Najeriya, wacce ta lashe kofin Afrika sau uku, tana matsayi na 39 a duniya a baya.

Super Eagles ta kuma tashi daga matsayi na shida zuwa na hudu a iya kwallo a nahiyar Afirka.

Super Eagles ta doke Libya da ci 1-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Afirka na 2025, wanda shi ne kadai wasan da suka yi a watan Oktoba.

An dage wasa na biyu da bangarorin biyu za su kara a Libya, baayn d Super Eagles ta janye daga wasan saboda korafin an yasar da su a filin jirgi, zargin da hukumomin Libya suka musanta.