Hukumar kwallon kafar Najeriya (NFF) ta bayyana cewar tawagar kasar “Super Eagles” ba zata buga wasanta da Libya ba a ci gaba da gasar cin kofin nahiyar Afrika, bayan da hukumomin kasar suka yi shagulatin bangaro da tawagar ta Super Eagles a filin saukar jiragen saman Al-Buraq tsawon fiye da sa’o’i 12 bayan data sauka a kasar.
Sanarwar da sashen yada labaran NFF ta fitar a yau Litinin, tace an yi watsi da tawagar a filin saukar jiragen saman na Al-Buraq.
Haka shima bidiyon da bangaren yada labaran tawagar ta Super Eagles ya wallafa ya tabbatar da hakan, inda ya nuna ‘yan wasan da masu horas dasu da kayayyakinsu a yashe a filin saukar jiragen saman, sannan ma’aikatan tashar jiragen saman na nuna halin ko in kula da halin da suke ciki.
Da safiyar jiya Lahadi ne tawagar Super Eagles ta tashi zuwa Libya, gabanin karawar da zasu yi da takwararsu ta “Mediterranean Knights” a ci gaba da gasar cin kofin nahiyar Afrika a ranar ta 4.
An tsara cewa kasar Libya zata karbi bakuncin tawagar da ta taba daukar kofin gasar nahiyar Afrika har sau 3 a filin wasa na “Shahidan Benina” dake garin Benina mai cin ‘yan kallo 10, 000, mai tazarar kilomita 10 daga Benghazi, amma rahotanni sun bayyana cewar an kada su zuwa wani birnin na daban.
Sanarwar ta kara da cewa ‘yan wasan sun yanke shawarar cewa ba zasu buga wasan ba, a yayin da jami’an NFF ke fafutukar samun jirgin da zai maido su gida.
Najeriya ta samu nasarar jefa kwallo daya mai ban haushi a ragar kasar Libya a karawar da suka yi a filin wasa na Godswill Akpabio dake birnin Uyo a Juma’ar da ta gabata sakamakon kwallon da dan wasa Fisayo Dele-Bashiru ya jefa ana daf da tashi daga wasa.
Dandalin Mu Tattauna